<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Hatton, John (1710-1793), Watts, Isaac (1674-1748)</author>
<title>Ya Almasihu, Mulkinka Zai Fi Duka LW35</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Almasihu, mulkinka
 Zai fi duk sauran mulkoki,
 Zai tabbata har abada,
 Madauwami ne mulkinka.

[V2]
 2) Ga ƙoshin rai a mulkinka,
 Albarka kuwa a yalwace,
 Ga ƙauna, murna, lafiya,
 Ga ƴanci kuma cikakke.

[V3]
 3) Yi yabonsa babu fasawa,
 Samari, yara, tsofaffi.
 Mulkinsa yana da girma fa,
 Sunansa kuwa mai tsarki ne.

[V4]
 4) Albarka ga Ubangiji,
 Mai mulkin dukan duniya.
 Ƴan Adam duk, ku neme shi
 Mai jinƙai ne har abada.</lyrics>
<hymn_number>35</hymn_number>
</song>